<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1)Duba, Yesu yana zuwa.
 Dā ya mutu dominmu,
 Dubban dubbai, tsarkakansa,
 Duka za su rako shi.
 Halleluya! Halleluya!
 Za ya nuna ikonsa.

[V2]
 2) Duk jama'a za ta gan shi,
 Su da suka soke shi,
 Cikin tsoro za su san shi,
 Ba sa so su tarbe shi.
 Suna kuka, suna kuka,
 Suna duban Sarkinsu.

[V3]
 3) Dā ya zo da kalmar ceto,
 Dā ya zo da gafara.
 Za ya komo mai shari'a,
 Za mu taru gabansa.
 Wa zai tsaya, wa zai tsaya
 Cikin ranar fushinsa?

[V4]
 4) Shi da kansa za ya sauko,
 Ranar fansarmu ta zo,
 Za mu tarbe shi a hanya,
 Masu rai da matattu.
 Cikin Sama, cikin Sama
 Za mu ga Ubangiji.

[V5]
 5) Zo da sauri, Almasihu,
 Masu Bi 'na jiranka.
 Ƙarfii mulki, ƙarfi yabo,
 Naka ne har abada.
 Halleluya! Halleluya !
 Zo da sauri, zo yanzu.</lyrics>
<title>Duba, Yesu Yana Zuwa LW120</title>
<hymn_number>120</hymn_number>
</song>